Obasanjo ne uban siyasar Najeriya – Shugaban jam’iyyar NUP

Obasanjo ne uban siyasar Najeriya – Shugaban jam’iyyar NUP

- Ciyaman na jam’iyyar NUP ya bayyana tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a matsayin zakin siyasa

- Opara yace duk dan siyasa ko jam’iyyar da bata nemi shawarar Obasanjo ba a bangaren harkokin siyasa ba tana cikin bata

- Opara yace, Obasanjo zaki ne a siyasa, saboda yayi mulki Najeriya sau uku kafin kafin ya dora Yar’adua a shekarar 2007

Mista Perry Opara ciyaman na jam’iyyar NUP ya bayyana tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a matsayin zakin siyasa,wanda yake taimakawa wurin samun nasara a zabe.

Opara yace, duk dan siyasa ko jam’iyyar da bata nemi shawarar Obasanjo ba a bangaren harkokin siyasa, tana cikin bata a zaben 2019.

Yace Obasanjo zakin siyasa ne wanda duk, dole a girmama tsohon shugaban kasar bisa ga gudunmuwar daya bayar a siyar Najeriya, yace gujewa shawarar tsohon shugaban kasar zai jawa dan takara ko jam’iyya faduwar zabe, a zaben shekarar 2019.

Opara yace, Obasanjo zaki ne a siyasa, saboda yayi mulki Najeriya sau uku kafin kafin ya dora Yar’adua a shekarar 2007, duk da kullin da mutane keyi amma sai da’Yaradua ya lashe.

Obasanjo ne uban siyasar Najeriya – Shugaban jam’iyyar NUP
Obasanjo ne uban siyasar Najeriya – Shugaban jam’iyyar NUP

Ya kawo Jonathan a shekarar 2011, kuma a kan dukkanin ra’ayoyin mutane, amma Jonathan yaci, duk da cewa bashi da tsari, kuma a zaben 2015, Obasanjo ya hade tare da Muhammadu Buhari, kuma ya kawo shi.

KU KARANTA KUMA: Ziyarar shugaban kasa Buhari jihar Legas ta kawo takura ga matafiya a jirgin sama

Abun tambaya anan shine, ko ‘yan Najeriya zasu cigaba da amincewa da Obasanjo duk da cewa wadanda ake ganin kamar ya kawosu ana ganin sun kasa.

Opara yace Obasanjo cigaban tattalin arzikin Najeriya shine kadai damuwarsa, kuma ya nunawa ‘yan Najeriya yanda ake mulki sau uku.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng