Aliyu Tafida tare da wasu mutane, a jihar Nasarawa, sun koma PDP daga APC
- Jigon jam'iyyar APC a jihar Nasarawa ya koma jam’iyyar PDP
- Tafida ya bayyana komawarsa PDP ne a gaban Ciyaman na kungiyar PDP
Aliyu Bala Ahmed Tafida, daya daga cikin jagororin APC a jihar Nasarawa, sun koma jam’iyyar PDP, tare da mabiyansa su 20,000.
Ahmed Tafida, ya bayyana kudurinsa na komawa PDP, a gaban Ciyaman na shuwagabannin Jam’iyyar ta PDP, Sanata Walid Jibrin; Ciyaman na yankin Arewa ta tsakiya na PDP Hon. Dakas Shan; Sanata Philips Gyunka; da kuma Hon. Frances Orogu.
Tafida shine yazo na biyu a zaben primary da akayi wadan marigayi Musa Baba Onwana, yayi nasarar zama dan majalisar zartarwa mai wakiltar mazabar Nasarawa/Toto.
Sanata Jibrin ya bayyana jin dadinsa bisa ga dawowar Tafida jam’iyyar tasu.
“Mu a PDP mun yadda cewa mulki na Allah ne, kuma shine ke bawa wanda yaso. Shiya bamu a da, kuma ya karba, amma muna ta kokarin shirya kanmu don samun nasara shekara mai zuwa”, inji shi.
KU KARANTA KUMA: ‘Yan Sanda Sun tabbatar da guduwar wadanda ake zargi Melaye ke basu makamai
Tafida ya nuna jindadinsa bisa komawa jam’iyyar ta PDP. “Nayi farincikin kasancewa a nan. Ina kuma farin ciki da kasancewa inda za’a daratani, a gode mani kuma a san girmana”.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng