Dapchi: Ka gaggauta daukar matakin ceto Leah - Afenifere da kungiyar kirista sun fadawa Buhari

Dapchi: Ka gaggauta daukar matakin ceto Leah - Afenifere da kungiyar kirista sun fadawa Buhari

- Kungiyar Yarabawa ta siyasa, Afenifere da na Kiristocin Najeriya, sunyi kira ga gwamnatin tarayya data gaggauta daukar mataki don ceto dalibar Dapchi data rage hannun ‘Yan Boko Haram

- Kungiyar ta Afenifere sunyi kira ga Majalisar Dinkin Duniya datayi bincike bisa ga kisan da Makiyaya keyi a fadin kasar nan

- Odumakin yace, sunabukatar gwamnatin tarayya datayi amfani da yarjejeniyar datayi don ceto ‘yan matan makaranta 111, don ceto yarinyar data rage a hannun ‘yan ta’addan

Kungiyar Yarabawa ta siyasa, Afenifere da Kiristanci ta Najeriya, sunyi kira ga gwamnatin tarayya data gaggauta daukar mataki don ceto dalibar Dapchi data rage hannun ‘Yan ta’addan Boko Haram, mai suna Leah Sharibu.

Kungiyar ta Afenifere sunyi kira ga Majalisar Dinkin Duniya datayi bincike bisa ga kisan da Makiyaya keyi a fadin kasar nan. Bukatar kungiyar ta Yarabawan, wadda Sakatarin hurda da jama’a na kungiyar, Mr. Yinka Odumakin, shine ya karantawa ‘yan Jarida.

Bayanin ya fito ne anyishi ne bayan taron wata wata da kungiyar keyi a gida shugabanta, Chief Reuben Fasoranti, a Akure, jihar Ondo, sai bayanin PFN yazo a wani jawabi mai dauke da sa hannun shugaban tarayya, Revd. Felix Omobude, a ranar Talata.

Odumakin yace, “Muna bukatar gwamnatin tarayya datayi amfani da yarjejeniyar datayi don ceto ‘yan matan makarantar 111, don ceto yarin data rage a hannun ‘yan ta’addan, Leah Sharibu, da kuma sauran ‘yan matan chibok da suka rage, a hannun wadanda ke rike dasu.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram: Majalisar dinkin duniya ta zuba N4n domin ceto rayuka a Arewa maso gabas

Gwamnatin Buhar bazata iya duka kirji ban a cewa tafi gwamnatin Jonathan, idan har yarannan na hannun ‘yan ta’adda”.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel