Na shafe fiye da shekaru 10 ba tare da kusantar iyali ba - Fasto

Na shafe fiye da shekaru 10 ba tare da kusantar iyali ba - Fasto

Babban limamin Cocin Christ Ambassadors Church International, Fasto Francis Gachieki ya bayyana cewa ya shafe sama da shekaru 10 ba tare da kusantar iyalin sa ba.

Shugaban Limaman dan kasar Kenya ya bayyana cewa, ba bu wani Zuhudu cikin wannan kaura da ya yiwa iyalin sa face wata rashin lafiya da ta sanya dole ya shafe wannan lokuta ba tare da gudanar da rayuwar sa yadda ta dace ba.

Francis yake cewa, ya kauracewa iyalin sa tun a shekarar 2007 sakamakon wata rashin lafiya mai sunan Prolactinoma da ta kashe kwayoyin halittar sa ma su sanya kwadayin 'ya mace.

Masana kiwon lafiya dai sun bayyana wannan cuta ta Prolactinoma da kashe kwayoyin sha'awar dukkan mai fama da ita, raguwar sunadarin Calcium daga cikin dan Adam, kashe kwayoyin halitta tare da tsiyayar ruwan mama ba tare da wani dalili ba.

Francis Gachieki
Francis Gachieki

Francis Gachieki
Francis Gachieki

Fasto Gachieki wanda mazaunin birnin Nairobi ne a halin yanzu yana neman taimako na tallafin kudi domin samun dama ta neman lafiyar sa a kasar Indiya, baya ga barar addu'o'in al'umma na samun waraka.

KARANTA KUMA: An samu sabanin ra'ayi tsakanin gwamnati da iyayen 'yan Mata kan koma wa makarantar Dapchi

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan cuta ta fara bayyana alamun ta kan babban Limamin tun bayan auren sa a shekarar 2002.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, majalisar dokoki ta sake jinkirta lokacin amincewa da kasafin kudi na shekarar 2018.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng