Annoba ta kashe mutane 8 a kano

Annoba ta kashe mutane 8 a kano

- Wata annoba ta aukawa kauyen Dungurawa, a karamar hukumar Dawakin Tofa, a jihar Kano, inda tayi sanadiyar mutuwar mutane takwas

- Mazauna garin sunce annobar ta fara ne satin da ya wuce, a kauyen, wanda ya tayarwa mutanen garin hankali

- Sunce wadanda suka rasa rayukansu sun hada yara ‘yan shekaru bakwai zuwa kasa da kuma matasa ‘yan shekaru 13 zuwa 25

Wata annoba ta aukawa kauyen Dungurawa, a karamar hukumar Dawakin Tofa, a jihar Kano, inda tayi sanadiyar mutuwar mutane takwas wanda suka hada yara kanana da kuma samari matasa.

Mazauna garin sun fadawa jaridar Nation, a ranar Litinin, cewa annobar ta fara ne satin da ya wuce, a kauyen, wanda ya tayarwa mutanen garin hankali, bisa ga yanda aka ringa mutuwa kusan kowace rana.Sunce wadanda suka rasa rayukansu sun hada da yara ‘yan shekara bakwai zuwa kasa da kuma matasa ‘yan shekara 13 zuwa 25.

Cutar a yanda mutanen garin suka fada, ta fara ne daga zazzafar masassara da ciwon kai da kuma ciwon ciki.

Annoba ta kashe mutane 8 a kano
Annoba ta kashe mutane 8 a kano

Akwai wanda ya rasa yara uku, cikin mazauna garin, Malam Suleiman Musa Tafida, yace dansa na uku ya rasu ne a yau da rana, bayan ya rasa wasu yaran biyu kafin shi, duk ta hanyar annobar. Sai Malam Haruna Abdullahi wanda shima ya rasa diyarsa a ranar Alhamis data gabata, sakamakon annobar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari ya nuna rashin yarda da Karin wa’adin jagorancin Oyegun

Dagacin kauyen, Malam Dahiru ya tabbatar aukuwar annobar, sun kuma sanar da hukumar lafiya ta karamar hukuma don ta nemar masu agaji daga gwamnatin jiha, akan annobar.

Anyi kokarin magana da kwamishinan lafiya na jiha Dr. Kabir Ibrahim Gwarzo amma abun ya gagara, sakamakon wayarsa na kashe.

A wani lamari na daban mun samu rahoton cewar an kashe mutum hudu daga cikin makiyayan a ranar Lahadi dinnan a karamar hukumar Guma da Agatu, yayinda aka sake kashe daya akan hanyar Makurdi, ranar Asabar din data gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng