Sauya fasalin zabe: Majalisan dattawa za ta sake gabatar da dokar
Majalisar dattawa Najeriya ta sake gabatar da takardan sauya fasalin dokar zaben hukumar INEC.
Za’a sake gabatar wannan sabon dokan yau Talata, 27 ga watan Maris, 2018. a filin majalisar dattawa da ke babban birnin tarayya, Abuja.
Gabanin majalisar dattawa, yan majalisan wakilai sun dade da sake gabatar da dokan a makon da ya gabata.
Yan majalisan za su sake gabatar da wannan zabe ne bayan shugaba Muhammadu Buhari ya yi watsi da dokar yayinda suka kai masa domin ya rattaba hannu a kai.
Yan majalisan suna kan bakansu cewa wajibi ne a a sauya fasalin zaben 2019. Masu sharhi sun bayyana cewa anyi wannan dokan ne domin musgunawa shugaba Buhari.
KU KARANTA: Buhari ya rattaba hannu kan yarjejeniya da kasar Switzerland kan dawo da kudaden Najeriya
Wannan abu ya jawo cece-kuce tsakanin yan majalisan da kuma yan Najeriya ga baki daya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng