Shugaba Buhari ya rattaba hannu kan yarjejeniya da kasar Switzerland kan dawo da kudaden Najeriya
Bayan amincewan majalisar zantarwan tarayya FEC, shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan takardu biyu.
Mai Magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana wannan ne inda yace shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan takardan yarjejeniya tsakanin gwamnatin Najeriya, gwamnatin kasar Switzerland da kungiyar dawo da kudaden sata domin dawo da kudaden Najeriya da wasu yan Najeriya suka kai kasar Switzerland.
Wanna mataki zai karawa Najeriya isassehn kudi domin aiwatar da ayyukan masu kyau da aka yiwa yan Najeriya alkawari.
KU KARANTA: Miyetti Allah sun kafa dokar ta baci a jihar Binuwai
Ya kara da cewa takarda na biyu da shugaba Buhari ya rattaba hannu kai shine na tsakanin gwamnatin Najeriya da Singapore kan dakile rashin biyan haraji da kuma zalunci kan haraji. Da wannan yarjejeniya, ana sa ran alakan kasuwancin Najeriya da kasar Singapore zai bunkasa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng