Hukumar ‘yan sanda na binciken jami’an Civil Defense bisa kisan matashi a kan satar mangwaro
Hukumar 'yan sandan na binciken mutuwar matashin, Luka Makana, da aka ce ya mutu ne sakamakon dukan wuce kima jami'an hukumar NSCDC suka yi masa.
Wannan lamarin ya faru ne a garin Bangi dake karamar hukumar Mariga ta jihar Neja.
Mahaifin Luka, Joseph Tanko, ya ce jami'an NSCDC sun kamo Luka ne daga daga daji bisa zarginsa da satar 'ya'ya'n mangwaro guda biyar. Ya kara da cewa, sun daure Luka a ofishinsu tare da lakada masa dukan da ya yi sanadiyar mutuwar sa.
Tanko ya cigaba da cewa, suna tsaka da neman matashin ne sai suka ga jami'an 'yan sanda na fitowa da gawar sa daga ofishin hukumar NSCDC. Da aka tambayi Tanko ko yana da tabbacin 'yan Civil Defence ne suka kashe Luka, sai ya ce, "daga ofis dinsu aka fito da gawar sa."
Kakakin hukumar 'yan sanda a jihar Neja, ASP Abubakar Dan Inna, ya tabbatar da afkuwar lamarin tare da tabbatar da cewar jami'an hukumar NSCDC din ake zargi da kisan Luka na tsare a hannunsu yayin da ake cigaba da gudanar da bincike.
DUBA WANNAN: Wuta tayi barna, ta kone daya daga cikin cibiyoyin bincike mafi amfani a arewacin Najeriya
Saidai kakakin hukumar NSCDC, Malam Ibrahim Yahaya, ya ce matashin ya mutu ne sakamakon ciwon ciki. A cewar sa, babu wanda ya doki Luka.
Rahotanni sun bayyana cewar wannan shine karo na uku da wani ya rasa ransa a hannun jami'an NSCDC a jihar Neja.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng