adda na matsawa 'yan Boko Haram har suka sako 'yan matan Chibok - Aisha Wakil

adda na matsawa 'yan Boko Haram har suka sako 'yan matan Chibok - Aisha Wakil

Fitacciyar matar nan da ake kyautata zaton tana daya daga cikin wadanda suka fi kusanci da 'yan kungiyar Boko Haram din nan ta ta'addancin mai suna Aisha Wakil da ake yi wa lakani da 'uwar 'yan Boko Haram' ta zayyana yadda ta shawo kan 'yan kungiyar har suka sako 'yan matan makarantar Dapchi da suka sace.

Hajiya Aisha tace tun bayan sace 'yan matan ne dai ta samu labarin a inda da kuma hannun wanda suke wanda hakan ne ma ya sanya ta shiga-ta-fita har sai da ta shawo kan su suka sako su.

adda na matsawa 'yan Boko Haram har suka sako 'yan matan Chibok - Aisha Wakil
adda na matsawa 'yan Boko Haram har suka sako 'yan matan Chibok - Aisha Wakil

KU KARANTA: Kalaman Buhari ne ke jaza kashe-kashe a Najeriya - Sule Lamido

Legit.ng ta samu cewa, a cewar ta bayyana cewa tayi ta ta basu hakuri ne sannan kuma taro hada su da Allah tana rokon su kan su duba girman Allah da na manzon sa su sako 'yan matan.

"Ana cikin haka ne ma sai 'yan Boko Haram din suka tabbatar mani da cewa in kwantar da hankali na za su sako 'yan matan ba da dadewa ba." Ta ce.

A wani labarin kuma, Fitaccen dan siyasar nan tsohon gwamnan jihar Jigawa sannan kuma mai takarar neman tikitin takarar kujerar shugaban kasar Najeriya a zabe mai zuwa na 2019 Alhaji Sule Lamido ya bayyana cewa ta wani bangaren kalaman shugaba Buhari ne ke haddasa ruruwar wutar rikicin kashe-kashen da ake fama da shi a Najeriya.

Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wata fira da yayi da wakilin majiyar mu ta Radiyo Faransa wadda kuma suka wallafa tare da watsawa a kafafen yada labaran su.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng