An binne tsohon ministan ayyuka Lawal

An binne tsohon ministan ayyuka Lawal

Rahotanni sun kawo cewa an binne Hassan Lawal, tsohon ministan ayyuka wanda ya rasu a ranar Lahadi a Abuja, a makabartan Kofsar Hausa dake Keffi, jihar Nasarawa.

Mohammed Auwal, babban limamin masallacin Keffi, wanda ya jagoranci sallar gawan, yayi addu’an Allah ya ji kan marigayin.

Mista Lawal wanda aka haifa a shekarar 1954 ya rasu yana da shekaru 64 a asibitin Turkish, Abuja da misalin karfe 4:30 na safe, a ranar 25 ga watan Maris, ya rasu ya bar matan aure biyu da yara shida.

An binne tsohon ministan ayyuka Lawal
An binne tsohon ministan ayyuka Lawal

A halin da ake ciki, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ta’aziyya ga jihar Nasara kan rashi da suka yi wanda ya bayyana a matsayin babban rashi ga kasar.

KU KARANTA KUMA: An gurfanar da wani mutun bisa zargin lalata nakasashiyar yarinya

Haka zalika gwamnan jihar Nasarawa, Tanko Almakura ya nuna jimami akan rasuwaar Missta Lawal cewa jihar zatayi kewan sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng