Muna sa ran Boko Haram za su dawo da daliba Leah yau – Sifeto Ibrahim Idris

Muna sa ran Boko Haram za su dawo da daliba Leah yau – Sifeto Ibrahim Idris

Babban sifeto janar na hukumar yan sanda, Ibrahim Idris, ya tabbatar da cewa yarinya mabiya addinin kiristan da ta rage a hannun yan Boko Haram za ta dawo gida yau.

Sifeton yan sandan ya bayyana hakan ne a shelkwatar rundunar sojin Operaton zaman lafiya dole da ke zaune a Maiduguri yayinda yake tafiye-tafiyensa na jihohin yankin Arewa maso gabas 3.

“Ya kamata in je Dachi yau amma saboda na samu labarin cewa da yiwuwan a dawo da Leah yau, na fasa tafiyan,”

“Abu ne na fahimta cewa a irin wannan hali da muke ciki, kada mu dau wani mataki da zai zama cikas ga nasarorin da aka samu."

“Kun san da jirgi mai saukan angulu nike yawo, kuma idan na shiga yankinsu, Boko Haram zasuyi tunanin cewa na saba alkawarin da akayi da su ne. Saboda haka na daga tafiyana”

Muna sa ran Boko Haram za su dawo da daliba Leah yau – Sifeto Ibrahim Idris
Muna sa ran Boko Haram za su dawo da daliba Leah yau – Sifeto Ibrahim Idris

Yan Boko Haram sunyi garkiwa da yan mata 110 a garin Dapchi ranan 19 ga watan Fabrairu, 2018.

A ranan Laraba, 21 ga watan Maris, sun sako 104 daga cikin yaran amma suka rike Leah saboda bata musulunta ba.

5 daga cikin yan matan sun rasa rayukansu yayinda suke hannun yan Boko Haram.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel