Darajar Naira ta karu bayan da CBN ya zuba $340 a kasuwar hada-hadar kudade
Babban bankin tarayyar Najeriya a ranar juma'ar da ta gabata ya sanar da zuba kudaden kasar waje na Dalar Amurka da suka kai $340 miliyan zuwa kasuwar hada hadar kudaden waje na Najeriya domin tabbatar da daidaituwar al'amurra.
Wannan dai ya fito ne daga bakin Daraktan bankin mai kula da harkokin yada labarai mai suna Mista Isaac Okorafor a cikin wata sanarwar da ya rabawa manema labarai.
KU KARANTA: Abu 11 da suka faru tun bayan sace 'yan matan Dapchi
Legit.ng ta samu cewa a satin da ya gabata ma dai babban bankin ya zuba dalar Amurka miliyan 210 a kasuwar canjin ta Najeriya.
Yanzu dai kamar yadda muka samu, ana sayen dalar Amurka daya ne akan Naira 362 a kayyadajen farashin gwamnati.
A wani labarin kuma, Rahotanni daga alkaluman da muke samu suna tabbatar mana da cewa gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta tattara akalla Naira Tiriliyan 8.9 tun bayan dabbaka yin anfani da asusun bai daya a watan Satumbar shekarar 2015.
Babban Akawun gwamnatin tarayyar ne dai Alhaji Ahmed Idris ya bayyana hakan a garin Abuja lokacin da yake gabatar da wata makala ga dandazon 'yan jarida da ke aika rahoto kan harkokin kudi.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng