Bayan kokarin addinin Islama na kore bambancin kabilanci, kamar dai musulmin duniya sun dawo dashi cikin rayuwarsu - Erdogan
- Erdogan na kokarin dawo da daular Islama wadda Turkiyya ta mulka bayan da Turai suka ki karbar kasarsa
- Yace hadin kan Musulmi ba zai yiwu ba sai sun daina banbanta kansu ta jinsi, kabila da darika
- Musulmin duniya sun kasa kansu kashi-kashi a yau
A kokarinsa na hado kanmusulmin duniya, shugaban Turkiyya, kuma tsohuwar uwar daular Islama ta Santambul, Rajab Dayyab Erdogan yace Musulmin duniya su suke lahanta kansu da kansu bayan da suka bambanta kansu ta fannin addini, kabila, bangare da ma alkibla.
A cewarsa dai, wannan shi ya hana mutum biliyan dake cikin addinin katabus, koda yake suna da yawan da zasu iya yi wa kansu kiyamul-laili.
Shugaban na Turkiyya, Recep Tayyip Erdoğan ya bayyana cewa,babu wata kasa a duniya da ta isa ta nuna wa Musulmai yatsa,idan har suka yi watsi da kabilanci don zama tsintsiya madaurinki daya.
DUBA WANNAN: Ta mutu garin soyayya a Otal, ya binne ta a daji
A yanzu dai musulmi sun koma bangarancin siyasa, kalar fata, addinanci, bautar da juna, kafirta juna, da ma kisan juna kan waye ke kan addinin na gaskiya, abu da ya yadu a tsakanin samari a ko'ina suke a duniya.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng