Abubuwa 11 da suka faru tun bayan sace 'yan matan Dapchi
Ko shakka babu kusan dukkan kafafen yada labaran cikin gida na kasar Najeriya sun raja'ane a satin da ya gabata ga labari batun maido 'yan matan makarantar kwana ta Dapchi da aka yi a ranar Laraba biyo bayan sace su da akayi a watan jiya.
Yayin da wasu ke ganin lamarin tamkar wasan kwaikwayo ne, wasu kuma jinjina suke ta yi ga gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari wajen ganin an maido 'yan matan ba tare da an cutar da su ba.
Legit.ng ta dan yi wani bincike da nufin yin waiwaye ga wasu daga cikin abubuwan da suka faru tun bayan sace 'yan matan a watan Fabreru.
KU KARANTA: Yan Boko Haram sun sako dayar dalibar da suka rike
1. A ranar 19 ga Fabrairu ne dai aka sace 'yan matan a makarantar su
2. Kuma dalibai 110 ne 'yan kungiyar ta Boko Haram suka sace
3. Abun da ya fi daure kai kuma shine cewar an sace su ne kwana daya bayan sojoji sun fice daga garin
4. Tabbas jama'a sun shiga rudani kan sace 'yan matan musamman ma iyaye da kuma iyalan su
5. Da farko dai da gwamnati ta ce 'yan matan sun shiga daji ne domin buya
6. Daga baya kuma bayan kimanin kwanaki 7 gwamnati ta amince an sace su
7. Haka zalika gwamnatin jihar Yobe ma ta yi ikirarin ceto 'yan matan, kafin daga baya ta karyata kan ta tare da neman afuwa
8. Kungiyar Boko Haram din dake karkashin ikon Abu Musab Al-Barnawi ne ake tunanin sun sace 'yan matan
9. Amma dai kungiyar ta ta'addancin Boko Haram ba ta fito ta yi ikirarin sace 'yan matan ba
10. Sace 'yan Matan Dapchi ya yi kama da yadda aka sace 'yan matan Chibok a shekarar 2014
11. Haka zalika hakan tamkar wata 'yar manuniya ce da cewar har yanzu Boko Haram barazana ce a duniya
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng