DA DUMUDUMINSA: Boko Haram Sun Sako Dalibar Dapchi Da Suka Rike Saboda Ta Ki Karbar Musulunci
- Boko Haram Sun Sako Dalibar Dapchi Da Suka Rike Saboda Ta Ki Karbar Musulunci
- 'Yan Boko Haram na kan hanyar su ta garin Dapchi don maido Kiristar da ta rage a hannun su
- Yanzu haka 'yan ta'addan na daf da garin na Dapchi
Labaran sirri da muke samu daga majiyar mu na nuni da cewa wasu daga cikin 'yan kungiyar nan ta ta'addancin Boko Haram da a watan jiya suka sace 'yan matan makarantar kwana ta Dapchi suka kuma maido da yawa daga ciki na kan hanyar su ta zuwa garin.
Kamar dai yadda muka samu a labarin da bamu gama tabbatar da sahihancin sa ba, mayakan na Boko Haram suna shirin maido dayar yarinya tilo kirista da suke cigaba da rikewa mai suna Sharibu Leah.
Legit.ng dai ta samu cewa majiyar ta kuma bayyana cewa yanzu haka 'yan ta'addan na daf da garin na Dapchi wanda hakan ne ma ya sanya matasan garin da dama ficewa daga garin domin gudun abun da ka-iya-zuwa ya dawo.
Asali: Legit.ng