Dan bautan kasa ya shiga matsala bayan yayiwa yar shekara 11 ciki (hotuna)

Dan bautan kasa ya shiga matsala bayan yayiwa yar shekara 11 ciki (hotuna)

- An kama wani dan bautan kasa bisa zargin yiwa yar shekara 11 ciki

- An rahoto cewa matashin na koyar da ita a gida lokacin da ya ci zarafinta

- An tattaro cewa yarinyar ta kasance dalibar JSS 2 a makarantar Nana College dake jihar Delta

An kama wani dan bautar kasa dake jihar Delta sannan an gurfanar da shi a gaban kotu bayan an zarge shi da yiwa wata yarinya ciki. An rahoto cewa matashin yayi wa yarinyar ciki sabanin koyar da ita da aka dauke shi yayi.

Wani mai amfani da shafin Facebook Isreal Joe ne ya wallafa labarin . a cewar Joe, dan bautan kasar yayiwa yar shekara 11 dake aji biyu na karamin sakandare ciki.

Joe ya bayyana cewa an dauki matashin ne domin ya koyama yarinyar darasi a gida. Ya kuma bayyana cewa ta ta kasance dalibar JSS 2 a makarantar Nana College dake jihar Delta.

KU KARANTA KUMA: Mutane 14 sun mutu sakamakon barkewar cutar amai da gudawa a Bauchi

A cewar sa, yan sanda na taimakawa sosai a bincikensu domin wanzar da adalci.

Ya kuma shawarci iyaye da su yi hankali da irin mutanen da suke dauka suna kula da yaransu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng