Mutane 14 sun mutu sakamakon barkewar cutar amai da gudawa a Bauchi
Billar cutar amai da gudawa yayi sanadiyan mutuwar mutane 14 a jihar Bauchi.
Kwamishinan lafiya na jihar, Dr Zuwaira Hassan ta bayyana haka a Bauchi a ranar Juma’a yayin zantawa da manema labarai kan al’amarin amai da gudawa da kuma zazzabin Lassa a jihar.
Ta ce mutane tara sun mutu daga cutar amai da gudawa yayinda biyar suka mutu daga zazzabin Lassa.
A cewar kwamishinar, an kwantar da mutane 26 a sashin da aka kebe na asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa Teaching Hospital (ATBUTH) Bauchi.
Dr Zuwaira ta sanar da cewa, wata daliba a makarantar kwalejin Kangere na daga cikin mutane tara da cutar ta sama.
KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa na amince a sulhunta da Boko Haram don sako 'yan matan Dapchi — Buhari
Ta daura alhakin billar wannan annoba akan rashin tsafta kamar bahaya a budaden waje da wasu ke yi.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng