Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari na ganawa da 'yan matan Dapchi da aka sako (Hotuna)
1 - tsawon mintuna
Labarin da muke samu yanzu yanzu da dumin sa na nuni ne da cewa Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari yanzu haka yana ganawa da 'yan matan Dapchi sama da dari da aka sako a ranar Larabar da ta gabata.
Mun samu dai cewa bayan yan Boko Haram din sun maido yan matan ne dai aka dauke su zuwa garin Maiduguri inda daga nan ne suka samu gwajin lafiyar su kafin daga bisani a dauko su cikin jirgi zuwa fadar shugaban kasar domin su gana.
Majiyar mu dai ta tabbatar mana da cewa Shugaba Buhari yana ganawa da su ne a babban dakin gabatar da taro n yan jarida na fadar ta sa.
Cikaken rahoton yana nan tafe.
Asali: Legit.ng