Kwamitocin bincike: Majalisar wakillai ta sake juyawa Shugaba Buhari baya
'Yan majalisar wakilan Najeriya a ranar Alhamis din da ta gabata sun saka alamar tambaya akan kwamitocin shugaban kasa ke fawa na binciken wasu badakalolin da ake zargin an tafka a gwamnatance inda suka bayyana su a matsayin masu shiga aikin wasu ma'aikatun gwamnati masu zaman kansu.
Tuni dai majalisar a karkashin jagorancin kakakin ta Yakubu Dogara ta amince da a gudanar da bincike kan lamarin da nufin lalubo hanya daya sahihiya da zata kawo karshen cin karo da junan da ake samu a dalilin hakan.
KU KARANTA: An rage kudin sadaki a jamhuriyar Nijer
Wannan dai kamar yadda muka samu ya biyo bayan wani kudurin da shugaban kwamitin majalisar a kan ansar koke-koken jama'a ta gabatar a zauren majalisar mai suna Mista Kingsley Chinda.
A wani labarin kuma, Wata kungiya da ta kira kanta ta jiga-jigan masu ruwa da tsaki da ma gudanarwar jam'iyyar APC ta yi kira ga shugabannin jam'iyyar a mataki na kasa da su hukunta dukkan wadanda suka kai jam'iyyar kotu ba tare da yin anfani da dukkan matakai na cikin gida ba game da batun karin wa'adin mulkin shugabannin ta.
Su dai wadanan 'yan kungiyar sun bayyana hakan ne biyo bayan wani zama na musamman da suka gudanar a garin Abuja inda kuma suka fitar da sanarwar bayan taro tare da bayyana matsayar su ga manema labarai.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng