An kama masu kai mata karuwanci kasashen waje a Najeriya

An kama masu kai mata karuwanci kasashen waje a Najeriya

- Rundunar 'yan sandan kasar Birtaniya wato Europol, ta bayyana cewar jami'an tsaro na kasa da kasa sun binciko wasu gungun masu aikata laifi a Najeriya.

- Masu laifin dai suna da wata kungiya mai suna The EIYE Brotherhood wadanda suke safarar mata a ciki da kuma wajen kasashen na turai.

An kama masu kai mata karuwanci kasar waje
An kama masu kai mata karuwanci kasar waje

Rundunar 'yan sandan kasar Birtaniya wato Europol, ta bayyana cewar jami'an tsaro na kasa da kasa sun binciko wasu gungun masu aikata laifi a Najeriya.

DUBA WANNAN: Kasar Isra'ila ta kama yaran Falasdin 562 ta kulle a kurkuku

Masu laifin dai suna da wata kungiya mai suna The EIYE Brotherhood wadanda suke safarar mata a ciki da kuma wajen kasashen na turai.

Hukumar ta Europol ta ce hadakar gwiwar kasashen Ingila, Spain da kuma kasar Najeriya, sannan kuma da wasu manyan hukumominc tsaro da abin ya shafa sune suka bankado wadannan mutane.

A yanzu haka dai an kama mutane kimanin 90, sannan aka kubutar da wasu mata da 'yan mata kimanin 39, wadanda aka tilastawa yin karuwanci a kasashen Turai.

Matan sun bayyana cewar sai da aka yi musu asiri mai karfi a Najeriya domin su bada hadin kai a fita dasu.

An kama masu laifin tun a watan Nuwambar bara, amma ba a saki bayanan ba sai a wannan lokacin, saboda gujewa masu katsalandan a harkar tsaro.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng