Da dumin sa: Ana dakun jiran isowar jiragen ruwa 33 makare da mai da abinci a Najeriya

Da dumin sa: Ana dakun jiran isowar jiragen ruwa 33 makare da mai da abinci a Najeriya

Mun samu labarin cewa yanzu zaman da ake yi kimanin jiragen ruwa manya ne kuda akalla 33 makare da kayan masarufi da suka hada da abinci da muka man fetur ne suka doso Najeriya ta tashar jiragen ruwa dake a birnin Legas.

Kamar dai yadda muka samu daga mahukuntan tashar jiragen ruwan, jiragen ana sa ran za su iso Najeriya ne a ranar 5 ga watan gobe.

Da dumin sa: Ana dakun jiran isowar jiragen ruwa 33 makare da mai da abinci a Najeriya
Da dumin sa: Ana dakun jiran isowar jiragen ruwa 33 makare da mai da abinci a Najeriya

KU KARANTA: Dapchi: Wallahi ba wasan kwaikwayo ne ba - Fadar Shugaban kasa

Legit.ng ta samu cewa daga cikin jiragen 33, 12 dukkan su dauke suke da man fetur yayin da sauran kuma ke dauke da sauran kayan masarufi da suka hada da Suga, kifi, takin zaman da dai sauran su.

A wani labarin kuma, Yau din nan da rana aka gudanar da wani babban taron masu ruwa da tsaki na majalisar tattalin arzikin kasar nan a babban dakin taro na fadar shugaban kasar Najeriya dake a garin Abuja a karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo.

Taron wanda ya samu halartar manya masu rike da mukaman da suka danganci tattalin arzikin kasar, ya kuma samu halartar fitattun masu kudin duniyar nan watau Bill Gates da kuma Aliko Dangote.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng