'Yan matan Dapchi: Wallahi ba wasan kwaikwayo bane - Fadar shugaban kasa

'Yan matan Dapchi: Wallahi ba wasan kwaikwayo bane - Fadar shugaban kasa

Babban mai taimakawa shugaban kasa na fuskar yada labarai Malam Garba Shehu ya maidawa jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) da ma sauran dukkan masu irin tunanin su na cewa sacewa tare da kuma maido 'yan matan Dapchi tamkar wasan kwaikwayo ne kawai.

Malam Garba Shehu ya bayyana cewa sam kwata-kwata ba wasan kwaikwayi ne ba illa dai kawai tsabar kwarewa ce a kan gudanar da mulki da har ya sanya aka maido su.

'Yan matan Dapchi: Wallahi ba wasan kwaikwayo bane - Fadar shugaban kasa
'Yan matan Dapchi: Wallahi ba wasan kwaikwayo bane - Fadar shugaban kasa

KU KARANTA: Kun san tsohuwar matar Dangote?

Legit.ng ta samu cewa Malam Garba Shehu haka zalika ya bayyana cewa kawai dai jam'iyyar ta Peoples Democratic Party (PDP) tana jin bakin ciki ne ganin yadda shugaba Muhammadu Buhari ya yi abun da jam'iyyar su da kuma tsohon shugaban kasa ya kasa yi lokacin da aka sace 'yan matan Chibok a shekarar 2014.

A wani labarin kuma, Mun samu labarin cewa yanzu zaman da ake yi kimanin jiragen ruwa manya ne kuda akalla 33 makare da kayan masarufi da suka hada da abinci da muka man fetur ne suka doso Najeriya ta tashar jiragen ruwa dake a birnin Legas.

Kamar dai yadda muka samu daga mahukuntan tashar jiragen ruwan, jiragen ana sa ran za su iso Najeriya ne a ranar 5 ga watan gobe.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng