Cigaba da riƙe wata dalibar Dapchi saboda kin shiga addinin Musulunci: Bala Lau ya mayar da martani
A ranar Laraba 21 ga watan Maris ne wasu mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram suka mayar da wasu daga cikin yan mata 110 dalibai sakandarin kimiyya na garin Dapchi dake jihar Yobe bayan kwashe kimanin wata guda a hannunsu.
Sai dai wasu rahotanni da Legit.ng ta samu sun tabbatar da cewar yan ta’addan sun ki sakin wata dalibar kwalejin mai suna Leah Sharibu, Kirista daya tilo dake cikin yan matan, saboda wai ta ki yarda ta sauya addininta daga Kiristanci zuwa Musulunci.
KU KARANTA: Barawon da ya sace biliyan 33 na yan fansho ya dawo da biliya 23 tare da fuskantar shekaru 6 a Kurkuku
Labarin wannaan yarinya ya watsu a shafukan sadarwa da dama, wanda hakan ya janyo cece kuce a tsakanin mabiya shafukan, inda mahaifiyarta da mahaifinta suka ce suna alfahari da wannan diyar tasu, saboda riko da addininta.
Sai dai a wata hira da yayi da BBC Hausa, shugaban kungiyar Izala, Sheikh Bala Lau ya mayar da martani game da wannan, inda yace yan ta’addan Boko Haram basa wakiltar Musulman Najeriya, ya kara da cewa karara sun yi hannun riga da musulunci.
Daga nan sai ya kara da cewa addinin Musulunci ya hana tursasa ma wani shiga addinin, inda ya kafa hujja da aya ta 256 na cikin suratul Baqara daga cikin Al-Qur’ani, inda Allah yayi hani da tursasa ma mutum a addini.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng