An kama wani matashi a jihar Zamfara yana sayar da kudin bogi

An kama wani matashi a jihar Zamfara yana sayar da kudin bogi

- Hukumar 'yan sandan Civil Defence sun kama wani matashi mai karancin shekaru a jihar Zamfara da laifin karbo kudin bogi daga hannun mai gidan shi yana sayarwa da jama'a, inda ya bayyana cewa a duk fitar da yayi mai gidan nashi yana biyan shi naira 2000

An kama wani matashi a jihar Zamfara yana sayar da kudin bogi
An kama wani matashi a jihar Zamfara yana sayar da kudin bogi

Jami'an hukumar Civil Defence sun kama wani matashi a jihar Zamfara da kudin bogi

A lokacin da suke tuhumar matashin a helkwatar su dake garin Gusau, shugaban hukumar na jiha David Abi, ya ce hukumar ta kama wanda ake zargin a karamar hukumar Maru da takardun 1000 kimanin guda 135 da kuma 500 guda 139, wanda hukumar ta tabbatar da cewa kudaden na bogi ne.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Bill Gates da Aliko Dangote domin walima a Aso Rock

Wanda ake zargin wanda ya ce sunan sa Mustapha Rabiu Maru, ya amsa laifin sa, inda ya tabbatar wa da hukumar cewa kudin na bogi ne, sai dai yana kaiwa wani mutum ne wanda ya bayyana sunan sa da Alhaji Sa'adu wanda shima yake hada kudin yana sayar wa jama'a.

Ya ce: "Wannan shine karo na hudu dana karbi kudin ina kaiwa jama'a, yanzu ma na karbo daga wurin Alhaji Sa'adu ne zan kaiwa Naibi. Sannan duk lokacin dana kai kudin yana biyana Naira dubu biyu."

Shugaban hukumar ya ce hukumar zata gurfanar da wanda ake zargin a gaban kuliya, sannan kuma zata yi kokarin kamo Alhaji Sa'adu wanda shine yake hada kudaden na bogi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng