Rundunar soji ta kama dan Boko Haram da ake nema ruwa a jallo
Dakarun Birgade 23 na Operation Lafiya Dole sun kama wani dan Boko Haram da ake nema ruwa a jallo, Bubayi Isa daga kauyen Panama, yankin Gundam, karamar hukumar Biu dake jihar Borno a jiya.
A wata sanarwa dauke das a hannun Birgediya Janar Texas Chukwu, daraktan labaran rundunar sojim ya bayyana cewa kamun ya biyo bayan wani farmaki.
Chukwu ya kara da cewa bincike ya tabbatar da cewa Bubayi ya kasance daya daga cikin yan ta’addan Boko Haram 37 da rundunar soji ta buga sunayensu.
Sauran da aka kama tare das hi sune Muhammad Buba da kuma Abdullahi Abubakar daga yankin yayinda Yakubu Abdullahi ya fito daga Sabon Gari Gado a karamar hukumar Bayo shima a jihar Borno.
KU KARANTA KUMA: Rigakafi yafi magani: An rufe makarantun kwana a jihar Borno
An kama yan ta’addan ne a kauyen Kalaa dake karamar hukumar Hong na jihar Adamawa.
Yan ta’addan sun amshi bakin cewa su yan kungiyar Boko Haram ne sannan sun bayyana irin ta’assar da sukayi bayan bincike da rundunar sojin ta gudanar.
A halin yanzu, gwamnatin jihar Borno ta bayar da umurnin rufe dukannin makarantun sakadare na kwana da ke wajen garin Maiduguri.
Hakan ya biyo bayan sace yan matan makarantar Dapchi da yan ta’addan Boko Haram suka yi a jihar Yobe.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng