Naji dadi da diya ta taqi karbar Musuluncin Boko Haram - Mahaifin kiristar Dapchi da Boko Haram suka mayar baiwa
- Nata Sharibu, baban dalibar Dapchi da ita kadai ta ta rage a ceto daga hannun ‘Yan kungiyar boko haram saboda taki yadda tayi ridda
- Daliban 110 ne aka kama lokaci da ‘yan ta’addan suka kai hari a Makarantar a ranar 19 ga watan Fabrairu
- Abun mamaki shine sai gashi ‘yan kungiyar ta boko haram sun mayar da ‘yan matan na Dapchi, a ranar Laraba
Naji dadi diyata batayi riddaba, inji baban Dalibar Makarantar Dapchi da ita kadai ta rage a ceto:
Nata Sharibu, baban dalibar Dapchi da ita kadai ta ta rage a ceto daga hannun ‘Yan kungiyar boko haram saboda taki yadda tayi ridda, sakamakon haka ‘yan kungiyar suka yanke shawarar cigaba da riketa a hannunsu.
Daliban 110 ne aka kama lokaci da ‘yan ta’addan suka kai hari a Makarantar a ranar 19 ga watan Fabrairu.
Abun mamaki shine sai gashi ‘yan kungiyar ta boko haram sun mayar da ‘yan matan na Dapchi, a ranar Laraba.
DUBA WANNAN: Awa daya Boko Haram suka yi a Dapchi suna wa'azi
Jaridar TheCable, tun farko ta bayyana cewa, Liya Sharibu, bata samu dawowa Dapchi ba, banda ‘yan matan makarantar biyar da aka samu labarin cewa sun rasa rayukansu.
Majiyoyi dayawa sun bayyanawa ‘yan jaridu cewa, ‘yan matan 104 ne aka saki, amma Lai Mohammed, Ministan Labarai, yace 76, ne kawai aka rubuta. Daga baya ya kara yawan ‘yan matan da aka saki zuwa 91.
Baban yarinyar ya bayyanawa RayPower jim kadan bayan samun labarin mayar da ‘yan matan Dapchi, cewa yaji dadi cewa diyarsa tana a raye, kuma yaji dadi dataki barin kiristanci kuma ya mata addu’ar dawowa lafiya.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng