Biki bidiri: Hotunan kyaututtukan da aka rabawa wadanda suka halarci bikin diyar Dangote
- Hotunan kyaututtukan da aka rabawa wadanda suka halarci bikin diyar Dangote
- Naira ta sha kashi a bikin da ya gudana a karshen satin da ya gabata
- Kayatattun akwatunan alfarma ne suka raba wa 'yan uwa da abokan arzikin su
Hakika ko shakka babu Naira ta sha kashi a bikin da ya gudana a karshen satin da ya gabata a tsakanin diyar shahararren mai kudin nan na Nahiyar Afrika watau Fatima Dangote da kuma angon ta kuma da ga tsohon Sifeto Janar na 'yan sandan Najeriya Jamil Abubakar.
KU KARANTA: Za'a soma hako mai a arewa
Sai dai har yanzu bayanai ne ke ta kara fitowa bayan na yadda bikin ya gudana inda muka samu cewa an raba kayatattun kyaututtuka ga dukkan wadanda suka je bikin.
Legit.ng ta samu dai cewa a maimakon robobi da sauran kyaututtukan da aka saba bayarwa a bikin sauran gama-garin mutane a matsayin kyauta ga mahalarta biki, su wadannan a bikin na su kayatattun akwatunan alfarma ne suka raba wa 'yan uwa da abokan arzikin su.
Mun samu dai cewa akwaitunan dai an kayatar da su sosai da fulawowi sannan kuma da tsadaddun kayayyakin da ba'a san ko menene ba a ciki wanda kuma aka hannata wa dukkan mahalarta taron.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng