Yanzu-yanzu: An damke babban dan Boko Haram a aka dade ana nema ruwa a jallo
-Hukumar sojin Najeriya ta damke kasurgumin dan Boko Haram
Hukumar sojin 23 Brigade na Operation LAFIYA DOLE sun cika hannu da babban dan Kungiyar Boko Haram da ake nema ruwa a jallo, Bubayi Isa, dan garin Panama, karamar hukumar Biu na jihar Borno a jiya Talata 20 ga watan Maris, 2018.
An damke shi ne tare wasu yaransa yan Boko Haram a kauyen Kalaa, karamar hukumar Hong a jihar Adamawa. Sauran sun bayyana cewa su mambobin kungiyar ne kuma suna da hannu cikin ayyukan kungiyar.
KU KARANTA: Buhari ya kure adaka; ba zai iya abin da ya wuce wannan ba - Shettima Yarima
Binicke ya nua cewa Bubayi Isa na ne lamba 37 a cikin jerin yan Boko Haram din da ake nema wanda hedkwatan hukumar soji ta wallafa. Wadanda aka kama tare da shi sune Muhammad Buba, Abdullahi Abubakar da Yakubu Abdullahi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng