Kungiyar Miyetti Allah ta daina bata sunan Fulani - Shugaban 'yan sanda
Rahotanni da sanadin jaridar Independent sun bayyana cewa, an nemi kungiyar Miyetti Allah da ta daina bata sunan Fulani tare da yi ma su bakin fenti domin hakan yana da nasaba ga wani mummunan sakamakon ga Fulani da ma ba a haifa ba.
A yayin ganawa da manema labarai a ranar Lahadin da ta gabata, babban sufirtanda na 'yan sanda James Vandefan, ya bayyana damuwar sa dangane da yadda ake dakilewa 'ya'yan Fulani neman ilimi a sanadiyar mummunan sakamako na jefa harkar fita kiwo.
Babban jami'in ya bayar da hujja ta cewa, makiyaya masu fita kiwo na janyo barazana ga rayuwar kananan yara da shekarun su ba su kai ba wajen wahalar da su a madadin sanya su a makarantu su nemi ilimi.
KARANTA KUMA: Sunadarin Vitamin D na dakile ciwon Zuciya - Bincike
Yake cewa, wannan lamari ya kan jefa yara cikin barazana daban-daban da ana iya magance su matukar an tanadi garkuna na kiwon shanu.
Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a wani sabon bincike da hukumar kula da harkokin kudi ta kasa ta fitar ya bayyana yadda wasu jihohi takwas ke sama ta fuskar kantar bashi da ya haura samun su na kudaden shiga.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng