Sarkin musulmi ya bukaci Shugaba Buhari ya farka daga doguwar sumar da yayi
Babbar kungiyar nan ta addinin Islama a Najeriya ta Jama’atu Nasril Islam, karkashin jagorancin Sarkin musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar III ya bukaci shugaba Muhammadu Buhari da ya farfado daga doguwar sumar da yayi domin ya cigaba da mulkin kasar nan yadda ya kamata musamman ma wajen fannin tsaro.
Wannan kiran dai kamar yadda kugiyar ta ayyana ya zama dole ne biyo bayan abun da ta kira kisan kiyashin da ake cigaba da yiwa musulmi a sassan kasar nan ciki hadda karamar hukumar Bassa ta jihar Filato.
KU KARANTA: Jam'iyyar APC na shirin watsewa a jihar Imo
Legit.ng ta samu cewa wannan kiran na kungiyar dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin ta ya fitar Dakta Khalid Abubakar Aliyu a garin Kaduna ya kuma rabawa manema labarai a Litinin din da ta gabata.
A wani labarin kuma, Wani babba kuma sanannen malamin addini dake shugabantar rukunin majami'u na Eternal Light of World Christian mai suna Dakta Adol Awam ya fito ya bayyana kudurin sa na neman tikitin takarar gwamnan jihar Ebonyi a zaben 2019 mai zuwa a karkashin jam'iyyar APC.
Kamar yadda muka samu, Awam ya bayyana kudurin na sa ne a garin Abakalki, babban birnin jihar ta Ebonyi a jiya Litinin yayin da yake zantawa da manema labarai.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng