Babban malamin addini ya shiga takarar tikitin zama gwamna a Najeriya

Babban malamin addini ya shiga takarar tikitin zama gwamna a Najeriya

Wani babba kuma sanannen malamin addini dake shugabantar rukunin majami'u na Eternal Light of World Christian mai suna Dakta Adol Awam ya fito ya bayyana kudurin sa na neman tikitin takarar gwamnan jihar Ebonyi a zaben 2019 mai zuwa a karkashin jam'iyyar APC.

Kamar yadda muka samu, Awam ya bayyana kudurin na sa ne a garin Abakalki, babban birnin jihar ta Ebonyi a jiya Litinin yayin da yake zantawa da manema labarai.

Babban malamin addini ya shiga takarar tikitin zama gwamna a Najeriya
Babban malamin addini ya shiga takarar tikitin zama gwamna a Najeriya

KU KARANTA: Gamayyar kungiyoyin kwadago na shirin shiga yajin aiki a Najeriya

Legit.ng ta samu cewa babban malamin ya kuma bayyana cewa ya yanke shawarar ya shiga siyasa ne domin tabbatar da samun shugabanci na garin ga al'ummar jihar wadanda yake da kudurin jagoranta indan har suka bashi dama.

A wani labarin kuma, Kakakin majalisar wakillai Mista Yakubu Dogara tare da hadin gwuiwar wani fitaccen shugaban kabilar yarbawa a karkashin inuwar kungiyar Yoruba Unity Forum mai suna Cif Dipo Jemileyin ya bayyana cewa shima yana goyon bayan a sake fasalin kasar nan a bangarori da dama.

Mista Yakubu Dogara tare Cif Dipo sun yi wannan kalaman ne a lokuta daban daban dukkan su yayin da suke gabatar da jawaban su a wajen wani taro da ake yi domin nemo hanyar tabbatar da cigaban kasar karo na uku a garin Abuja da wata kungiyar mai rajin kare dimokradiyya a Nahiyar Afrika ta shirya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng