Sabuwar Jami'ar Sojoji ta Biu zata dauki dalibai
- Matsalar tsaro a kasar nan ba abu bane sabo musamman ma a yankin Arewa maso Gabas, wanda 'yan ta'addan Boko Haram suke cin karen su ba babbaka, hakan ne ma ya saka gwamnatin tarayya ta dauki kudurin kaddamar da jami'ar sojoji a yankin.
Hukumar jami'ar soji da ake so a bude a Najeriya ta ce, zata dauki kashi 75 na farar hula, inda zata cike sauran kashi 25 din da sojoji.
DUBA WANNAN: Christiano Ronaldo yayi Allah wadai da irin azabar da ake yiwa mutanen kasar Siriya
Shugaban kungiyar fafutukar ganin an kaddamar da makarantar, Manjo Janar Mathias Efeovbokhan (rtd), wanda ya jagoranci 'yan kungiyar suka kaiwa ministan cikin gida, Abdulrahman Dambazau ziyara a jiya, ya bayyana cewa jami'ar tana da wasu ka'idoji wanda suka sha banban da na sauran makarantun soji na kasar nan.
Ya ce: "Jami'ar zata zamo abar alfahari a kasar nan, zata yi kokari wurin ganin ta samar da dalibai masu hazaka ta kowanne fanni."
Sannan ya kara da cewa jami'ar wacce ake so a gina ta a karamar hukumar Biu dake jihar Borno, zata zamo ta daya ta fannin yaye dalibai masu ilimi, sannan ya kara da cewar jami'ar baza ta yarda da tsarin kungiyoyi irin su ASUU ba.
Sannan ya tabbatar da cewar za a samar da tsaro sosai saboda dalibai dama ma'aikatan jami'ar, domin gudun barazanar 'yan ta'addan Boko Haram dake jihar.
A karshe ministan cikin gida Abdulrahman Dambazau ya nuna goyon bayan shi sannan ya tabbatar da cewar gwamnati zata yi maraba da jami'ar.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng