Tsaka-mai-wuya: Matasa sun yi wa Gwamna Badaru na Jigawa ihu a wajen taro

Tsaka-mai-wuya: Matasa sun yi wa Gwamna Badaru na Jigawa ihu a wajen taro

Zababben gwamnan jihar Jigawa dake a arewa maso yamma Alhaji Mohammed Badaru Abubakar a jiya ya so ya ji kunya a wani taron siyasa bayan da matasa a wajen suka rika yi masa ihu a yayin da yaje karbar wasu 'yan jam'iyyar adawa na PDP ya zuwa APC a jihar a karamar hukumar Birnin Kudu.

Kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu, dakin taron ya harmutse ne yayin da Gwamnan ya anshi abun magana zai soma bayanin sa sakamakon ihu da matasa suka rika yi masa wanda yayi sanadiyyar dakatar da jawabin na sa.

Tsaka-mai-wuya: Matasa sun yi wa Gwamna Badaru na Jigawa ihu a wajen taro
Tsaka-mai-wuya: Matasa sun yi wa Gwamna Badaru na Jigawa ihu a wajen taro

KU KARANTA: Tsintsiya ta kama hanyar watsewa a jihar Imo

Legit.ng ta samu cewa gwamnan ya je karamar hukumar ne domin ya kaddamar da wasu ayyukan raya kasa da dan majalisa mai wakiltar mazabar Birnin Kudi/Buji Magaji Da'u Aliyu ya assasa da suka hada da shinfida hanyar karkara da kuma bayar da tallafi ga matasa.

A wani labarin kuma, Shugabannin jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC) da sauran masu ruwa da tsaki sun soma wani shirin sasanta bangaren zartarwa da shugaba Muhammadu Buhari ke jagoranta da kuma bangaren 'yan majalisu da Sanata Bukola Saraki ke jagoranta.

Wannan dai matakin da suka dauka kamar yadda muka samu ya biyo bayan takun sakar da yanzu haka ake samu tsakanin bangarorin biyu musamman ma wajen tirka-tirkar sauya jadawalin zabe mai zuwa inda 'yan majalisun suka sha alwashin zartar da dokar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng