Hukumar 'yansanda ta mayar wa da Buhari martani kan bincikar IGP da 'tserewa' daga jihar Benuwe

Hukumar 'yansanda ta mayar wa da Buhari martani kan bincikar IGP da 'tserewa' daga jihar Benuwe

- Hukumar ‘Yan Sanda da Fadar Shugaban Kasa, ba water takadar bincike da aka ba Shugaban ‘Yan Sanda

- Duk wanda yace shugaban kasa ya bawa shugaban ‘Yan Sanda takardar bincike to ya kawo mana do mu nuna

- Hukuma ‘Yan Sandan a ranar Asabar, ta karyata maganar da ma’aikatan fada shugaban kasa sukayi aka cewa shugaba Muhammadu Buhari ya bawa shugaban ‘Yan Sandan takardar bincike

- Sakamakon rashin biyayya ga umurnin shugaban kasa dayace ya koma jihar Binuwai, bayan kisan da akayi na ranar farko ta sabuwar shekara

Hukumar 'yansanda ta mayar wa da Buhari martani kan bincikar IGP da 'tserewa' daga jihar Benuwe
Hukumar 'yansanda ta mayar wa da Buhari martani kan bincikar IGP da 'tserewa' daga jihar Benuwe

Hukuma ‘Yan Sandan a ranar Asabar, ta karyata maganar da ma’aikatan fada shugaban kasa sukayi aka cewa shugaba Muhammadu Buhari ya bawa shugaban ‘Yan Sandan takardar bincike, sakamakon rashin biyayya ga umurnin shugaban kasa dayace ya koma jihar Binuwai, bayan kisan da akayi na ranar farko ta sabuwar shekara a jihar.

“Babu wata takardar bincike da aka baiwa shugaban ‘Yan Sanda,” Jimoh Moshood, Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda, wanda ba’a dade da kara masa girma ba, ya tabbatarwa jaridar THISDAY a wayar salula, ya kara da cewa: “A Bayyane abun yake na cewa babu wata takardar bincike da aka bashi daga shugaban kasa”.

Shugaban kasar, bayan kisan mutane 73 da Makiyaya sukayi a kananan hukumomin Guma da Logo, jihar Binuwai, a ranar sabuwar shekara, ya umurci shugaban Jami’an ‘Yan Sandan daya koma jihar dake fuskantar wannan matsala don hana cigaban wannan kashe-kashe da kuma kawo kwanciyar hankali da zaman lafiya.

Amma shugaban kasar ya samu labari daga Gwamnan jihar, Dr Samuel Ortom, da kuma Dattawan jihar, lokacin daya kai ziyarar gaisuwa a Makodi, Birnin jihar, satin daya wuce, cewa shugaban ‘Yan Sandan ya sabawa umurninsa, sunce, Idris, ko kwana daya baiyi ba a jihar, saidai kawai ance yayi wuni daya a Binuwai, daga nan ya koma jihar dake makwabtaka da Binuwai, jihar Nasarawa, inda daganan ya koma Birnin Tarayya.

DUBA WANNAN: NCC ta kama tashar bogi ta N36m

“Bansan cewa shugaban ‘Yan Sandan bai zauna a jihar ba. Yanzu nake sanin haka a wannan taron. Nayi mamaki,” cikin jin kunya Buhari ya fadawa jama’ar dake taron, wadanda ke cikin fushin cewa kamar shugaban kasar na nuna rashin damuwa akan al’amarin nasu, saboda rashin zuwansa jihar sai bayan watanni biyu da faruwar al’amarin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng