Za'a tafi kotu tsakanin gwamnatin Tarayya da Kamfanunuwan wutar lantarki

Za'a tafi kotu tsakanin gwamnatin Tarayya da Kamfanunuwan wutar lantarki

- Rashin lantarki ya ki ci yaki cinye wa

- Fashola zai kai GEnCos kotu

- Kan batun kudaden samar da wuta N700b na NBET ake rigimar

Za'a tafi kotu tsakanin gwamnatin Tarayya da Kamfanunuwan wutar lantarki
Za'a tafi kotu tsakanin gwamnatin Tarayya da Kamfanunuwan wutar lantarki

Tun bayan da gwamnatin Najeriya ta sayar da NEPA a 2005 ake samun takun saqa tsakanin gwamnatin da 'yan kasuwar da suka sayi kamfanunuwan da aka farfasa gida-gida. Wannan karon rigimar na tsakanin gwamnati ne da GEnCos.

Su dai GenCos sune Generation Companies, wadanda su ke samar da wutar ta NEPA, inda sukan mikawa TCN, watau masu yawo da layukan wuyar a daji da birane, sai kuma DisCos, watau masu sayar da wutar a kauyuka da birane da masar kudin wata-wata.

Sai kuma NERC, wadanda su ke duba dokoki da lasisin wutar don kar wani ya kwari wani tsakanin Gwamnati, Yankasuwa da talakawa.

DUBA WANNAN: Nayi rawar gani - Sarki SLS II

Har yanzu dai ana takaddama kan kudin NBET, watau hukumar da asusun ta ke sammar da sabbin kudade don samar da wutar, wanda a kwanan nan kudin suka kai N700b, wanda ake ta cewa sun bace ne, amma Ministan wutar Fashola yace sam suna nan.

A yanzu dai Fashola yace a hadu a kotu, bayan da su GenCos din ke barazanar zuwa kotu kan ina kudaden suka buya, kumma menene kason su a ciki?

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng