Kwallo: Salah zai iya maye gurbin Messi a matsayin uban zura kwallo a raga

Kwallo: Salah zai iya maye gurbin Messi a matsayin uban zura kwallo a raga

- Masoya kwallon kafa sun rabu kulob zuwa kulob

- Wasunsu suna ganin daga Messi wasa ya tashi

- Sabon yayi Salah na kokarin shafe tutar Messi

Kwallo: Salah zai iya maye gurbin Messi a matsayin uban zura kwallo a raga
Kwallo: Salah zai iya maye gurbin Messi a matsayin uban zura kwallo a raga

Kocin Liverpool Jurgen Klopp yace Mohammed Salah na kan hanyar zama shahararren dan wasa kamar Lionel Messi bayan da ya zura wa Watford kwallo 4 a jiya Asabar.

Salah ne dan wasan da ke kan gaba a yawan kwallaye a dukkan manyan lig-lig guda biyar na Turai - inda ya tsere wa Lionel Messi na Barcelona da Harry Kane na Tottenham.

Amma klopp ya ce Salah mai shekara 25 da haihuwa ba ya damuwa da abin da wasu 'yan wasan ke yi:

"Ba na jin Mo na son a rika kwatanta shi da Lionel Messi".

DUBA WANNAN: Manyan mukarraban APC a wani sabon matsayi

A zagayen bana na wasannin dai, musulmin dan wasan ya taka leda ta gani ta fada inda ko 'yan hamayya sai da suka sara masa, kuma ga alama likkafarsa gaba-gaba take yi, musamman ganin yaro ne wanda da sauran shekarun wasa a kafarsa.

Wasan kwallon kafa dai a zamanin nan yafi komai kawo kudi musamman a kasashen turai inda abin ya zama kamar addini, kudaden da ake samarwa daga wasan sun hada da kwallon kafar kanta, talla, caca, cinikayyar 'yan wasa da ma sufuri da otal.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng