Buhari ya nada manyan mukarraban gwamnatinsa a wani sabon matsayi
- Buhari ya bawa Abba Kyari, Boss Mustapha, Emefiele, Lawal Daura, da wasu mutane 17, sabon matsayi
- Kwanaki bayan bayyana kudirin Gwamnatin Tarayya na kafa Kwamitin Tsaro na kasa, Shugaba Muhammadu Buhari, ya amince da tsarin Majalisar Wakilai
- Majalisar wadda shugaban kasa zai Jagoranta, za’a kaddamar da ita a ranar Litinin
Kwanaki bayan bayyana kudirin Gwamnatin Tarayya na kafa Kwamitin tsaro na kasa, Shugaba Muhammadu Buhari, ya amince da tsarin Majalisar Wakilai.
Majalisar wadda shugaban kasa zai jagoranta, za’a kaddamar da ita a ranar Litinin. Wadanda zasu zamo cikin mambobinta sun hada da Gwamnonin kebbi (Abubakar Bagudu), Taraba (Darius Dickson Ishaku), Filato (Simon Lalong), Legas (Akinwumi Ambode), Ebonyi (Dave Umahi), da kuma Dalta (Ifeanyi Okowa).
Saura sun hada da Sakataren Gwamnatin Tarayya (Boss Mustapha); Shugaban Ma’aikata na Shugaban Kasa (Abba Kyari); mai bawa shugaban kasa shawar ta fannin tsaro (Babagana Monguno), da kuma Ministoci bakwai.
Ministocin sun hada da Ministan Gona da Cigaban Birane (Audu Ogbeh); na Kudi (kemi Adeosun); na Al’amuran Cikin Gida (Abdurrahman Dambazau); na Kula da Kamfaninnika da kasuwanci (Okechukwu Enelamah); na Albarkatu na Ruwa (Suleiman Kazaure); na Muhalli (Ibrahim Jibrin); dana Bajat da Tsarin Mulki (Udo Udoma).
Kwamitin Tsaro na Abinci shugaban masu kariya (General Abayomi Gabriel Olonisakin); Gwamnan Bankin Najeriya (Godwin Emefiele); Shugaban Daraktoci na Sashen Kasuwanci (Lawal Daura), da kuma Hukumar Tsaro ta Kasa (Ahmed Abubakar), da kuma Babban Kwantroler Janar na Hukumar Harkokin Shige da Fice a Najeriya (Mohammed Babandede).
DUBA WANNAN: Shin mace zata iya sarautar Kano
Manufofin Majalisar zasu hada da, samar da mafita ga fada tsakanin Makiyaya da Manoma, Canjin Yanayi, Sauyin wurin Noma, yankunan Kiwo da Tafkuna, Koguna da sauran yankunan Ruwa; ragowar Man Fetur da tasirinsa a Yankin Kudancin Nijar Dalta; Cibiyoyin bincike na aikin noma da kuma ayyuka na tsaro da kuma safarar kaya ta barauniyar hanya.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng