Sanya wa jariri suna Donald Trump ya jawo cece kuce a kasar Afghanistan
- A can kasar Afghanistan wani dan kubulbulin yaro na can ya tada hatsaniya kan sunansa 'na kafirai' da aka sanya masa tun yana jariri.
- Jariri Donald Trump yaja hankali a kasar Afganistan
- Yaron da iyayensa sukasa masa sunan attajirin dan kasuwar nan, shugaban kasar Amruka da niyyar ya sake samun nasarar komawa shugaban kasa
A can kasar Afghanistan wani dan kubulbulin yaro na can ya tada hatsaniya kan sunansa 'na kafirai' da aka sanya masa tun yana jariri. Jariri 'Donald Trump' yaja hankali a kasar Afganistan.
Yaron da iyayensa suka sa masa sunan attajirin dan kasuwar nan, shugaban kasar Amurka. Iyayen yaron wadanda suka nuna kansu a matsayi ‘yan Amruka, sun shiga bakin mutane na maganganu na zagi akan sunan dansu na uku.
Wasu abun har ya kaiga yiwa Sayed barazanar kisa, wasu kuma sun zargeshi da jefa rayuwar yaron a hatsari sakamakon sunan da ya sanya masa. Sarai ustazai na Taliban ko ISIS na iya kisan wannan yaro kawai saboda sunansa.
Yaron da iyayensa sukasa masa sunan attajirin dan kasuwar nan, shugaban kasar Amruka da niyyar ya sake samun nasarar komawa shugaban kasa. Amma yanzu yana tsakiyar cibiyar watsa labaru da jama’a a Afganistan, bayan bayanin da aka dora game dashi a kafar sadarwa ta facebook.
DUBA WANNAN: Hukumar INEC na neman yadda aka yi zaben da kananan yara a Kano
Mutumin da ya nuna kansa a matsayin dan kasar Amruka, wanda ya jagoranci duniyar ‘yanci, Sayed Assadullah Pooya, yace, shi da matarsa sun shiga bakin jama’a da maganganu na zagi akan sunan da suka sanyawa yaronsu na uku.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng