Yace macizai abokansa ne, amma daya ya kashe shi murus

Yace macizai abokansa ne, amma daya ya kashe shi murus

- Dan kasar Malaysia din nan da ya yi suna saboda basirarsa ta iya wasa da macizai ya mutu bayan wata kububuwa ta sare shi

- Abu Zarin Hussin, wanda ma'aikacin kashe gobara ne, ya yi fice ne bayan wasu jaridun Burtaniya sun wallafa labaran da ke cewa shi dan kasar Thailand ne da ya auri macijiya

- Mr Hussin ya bai wa sauran ma'aikatan kashe gobara horo kan yadda za su iya sarrafa macizai

Yace macizai abokansa ne, amma daya ya kashe shi murus
Yace macizai abokansa ne, amma daya ya kashe shi murus

Wani saurayi da yayi suna wajen wasa da maciji a kasashen Asiya mai suna Abu Zarrin Husain ya rasu ranar litinin bayan da aka kwantar da shi a asibiti bayan macijiyar ta sare shi lokacin da suke aikin kama macizai.

Ya dai yi fice ne bayan wasu jaridun Burtaniya sun wallafa labaran da ke cewa shi dan kasar Thailand ne da ya auri macijiya kuma yake son macizai.

Dan kasar Malaysia din nan da ya yi suna saboda basirarsa ta iya wasa da macizai ya mutu bayan wata kububuwa ta sare shi a yayin wasanninsa.

DUBA WANNAN: Shin mace zata iya sarautar Kano

Dama dai akance ba'a sabawa da maciji, domin duk inda ka kai ga saboo dashi, wataran zai kaika ya baro.

Kasashen Asiya dai da na Afirka na fama da macizai musamman kububuwa, watau Cobra, wadda dafinsu kan kashe babban mutum cikin sa'a hudu idan babu kulawar asibiti ko kwararru.

Wasu masu wasa da maciji dai kan yi kurin sun sha maganin macijin amma abun da ke faruwa zahiri bai wuce sun iya juriya bane, ko kuma sun karye fiqar macijin domin ko da ya sari mutum hakoransa bazasu fasa fata ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng