Yanzu-Yanzu: Allah ya yi wa Sanata Ali Wakili na jihar Bauchi rasuwa
- Sanata Ali Wakili ya rasu
- Sanatan na wakiltar mazabar yankin majalisar dattijai ta jihar Bauci ta Kudu
- Mun dai samu labarin hakan ne daga Saleh Shehu Ashaka
Labarin da ke iske mu yanzu yanzu na nuni ne da cewa Sanatan dake wakiltar mazabar yankin majalisar dattijai ta jihar Bauci ta Kudu watau Sanata Ali Wakili rasuwa.
KU KARANTA: EFCC ta yi ram da wani babban jami'in gwamnatin jihar Borno
Mun dai samu labarin hakan ne daga majiyar mu ta wani shahararren mai sharhi akan lamurran yau da kullum a kafar sadarwar zamani ta Tuwita watau Saleh Shehu Ashaka kamar dai yadda ya ayyana a shafin na sa mai adrreshin @AshakaSaleh da safiyar yau.
Legit.ng ta samu cewa shi dai Sanata Wakili an haifeshi ne a shekarar 1960 inda kuma yayi karatun Firamaren sa a makarantar Lere sannan kuma ya je makarantar Damaturu inda yayin Sakandare.
Haka ma dai mun samu cewa yayi karatun jami'ar sa ne a jami'ar Bayero dake Kano sannan kuma tsohon jami'in Kwastam ne kafin daga bisani ya shiga harkar siyasa a shekarar 2015.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng