Jerin jihohi 16 na da ke fuskantar barazanar yunwa a Najeriya

Jerin jihohi 16 na da ke fuskantar barazanar yunwa a Najeriya

Manyan hukumomin dake kula da yalwatar abinci na duniya sun yi kakkausan gargadin yiwuwar samun matsalar yunwa matsanciya sakamakon karacin abinci da za ta iya shafar akalla kusan mutanen da suka kai miliya 4 dake zaune a jihohi 16 na arewacin Najeriya.

Kamar yadda muka samu, hukumomin abinci da kuma bunkasar aikin gona mallakin Majalisar Dinkin Duniya wata FAO a takaice da kuma wata hukumar ta bayar da agajin abinci ta Majalisar Dinkin Duniya din watau WFP sun ce matsalar za ta iya shafar garin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

Jerin jihohi 16 na da ke fuskantar barazanar yunwa a Najeriya
Jerin jihohi 16 na da ke fuskantar barazanar yunwa a Najeriya

KU KARANTA: Zaben 2019: Matasan Najeriya sun ce sai Dankwambo

Legit.ng ta samu cewa jihohin da hukumomin na FAO da kuma WFP suka zayyana a matsayin wadanda ke cikin hadarin sun hada da Niger, Kebbi, Katsina, Kaduna, Bauchi, Benue, Gombe, Zamfara, Sokoto, Kano, Yobe, Borno, Jigawa, Plateau, Taraba da kuma Adamawa.

A wani labarin kuma, Shugaban jam'iyyar adawa a jihar Kwara ta Peoples Democratic Party, Cif Iyiola Oyedepo ya sanar da cewa jam'iyyar ta sa ta karbi akalla magoya baya 800 daga jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress cikin 'yan kwanaki kadan da suka wuce.

Shugaban jam'iyyar dai Cif Iyiola shine ya sanar da hakan a yayin da yake zantawa da majiyar mu a garin Ilorin, babban birnin jihar Kwara a ranar Juma'ar da ta gabata inda kuma ya bayyana cewa wani babban dan siyasa ne Dakta Hanfi Alabere ya jagoranci magoya bayan.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng