Sauya sheka: Jam'iyyar PDP tayi wa APC jina-jina a jihar Kwara
Shugaban jam'iyyar adawa a jihar Kwara ta Peoples Democratic Party, Cif Iyiola Oyedepo ya sanar da cewa jam'iyyar ta sa ta karbi akalla magoya baya 800 daga jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress cikin 'yan kwanaki kadan da suka wuce.
Shugaban jam'iyyar dai Cif Iyiola shine ya sanar da hakan a yayin da yake zantawa da majiyar mu a garin Ilorin, babban birnin jihar Kwara a ranar Juma'ar da ta gabata inda kuma ya bayyana cewa wani babban dan siyasa ne Dakta Hanfi Alabere ya jagoranci magoya bayan.
KU KARANTA: Karin wa'adin mulki: Matasan APC sun yi fito-na-fito da Oyegun
Legit.ng ta samu cewa haka zalika shugaban jam'iyyar a jihar ya bayar da tabbacin cewa a shirye suke su karbi mulki daga hannun 'yan APC a jihar idan zaben 2019 ya zo.
A wani labarin kuma, Manyan hukumomin dake kula da yalwatar abinci na duniya sun yi kakkausan gargadin yiwuwar samun matsalar yunwa matsanciya sakamakon karacin abinci da za ta iya shafar akalla kusan mutanen da suka kai miliya 4 dake zaune a jihohi 16 na arewacin Najeriya.
Kamar yadda muka samu, hukumomin abinci da kuma bunkasar aikin gona mallakin Majalisar Dinkin Duniya wata FAO a takaice da kuma wata hukumar ta bayar da agajin abinci ta Majalisar Dinkin Duniya din watau WFP sun ce matsalar za ta iya shafar garin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng