Son mulki ya sa Yarima Salman yi wa mahaifiyar sa daurin talala
Kamar dai yadda muka samu daga kafafan yada labarai na kasar Amurka shine cewar, babban dan Sarkin Saudiya kuma Yarima mai jiran gadon masarutar, Muhammad Bin Salman ya yi wa mahaifiyarsa daurin talala.
A cewar majiyar ta mu ta NBC, yariman wanda yanzu yake da shekaru 31 a duniya ya yi hakan ne saboda mahaifiyar ta sa ta na kawo masu cikas wajen cikar burin na sa na zama Sarkin kasar wanda hakan ne ma ya sa yake tsoron kar ta shawo kan mahaifinsa wajen maye gurbinsa da daya daga cikin kannen sa.
KU KARANTA: Kasar Faransa ta bayar da umurnin a kamo diyar Sarki Salman
Legit.ng ta samu cewa yanzu haka dai hatta Sarkin daular Salman bai san ida dan nasa ya kai mahaifiyar ba lamarin da ya jefa zukatan jama'a da dama a masarautar cikin fargaba.
Haka ma dai kasar Saudiyya ta bayar da sammacin dakumo, Hussat Salman, diyar sarkin kasar Saudiyya, Sarki Salman.
Kasar Faransa ta bayar da umarnin cafke gimbiya Hussat ne bayan ta bawa wani dogarinta umarnin dukan wani hadiminta a gidanta na Faransa.
A kwanakin baya mun kawo ma ku rahoton wakilan gwamnatin Saudiyya da su ka ziyarci ma'aikatar tsaro ta Najeriya domin bayar da agajin kudi da kayan aiki ga gwamnatin Najeriya.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng