An fara samun sakonni daga Sambisa ta wayar wata budurwa da suka tafi da ita bayan harin Rann

An fara samun sakonni daga Sambisa ta wayar wata budurwa da suka tafi da ita bayan harin Rann

- Anyi amfani da wayar hannu ta salula ta daya daga cikin matan da ‘yan Boko Haram suka sace, an tura sako mara dadi ga lambobin cikin wayar.

- Hauwa Liman, wadda aka dauka ma’akaciyar hukumar bada taimakon farko ga marasa lafiya ce, wadda ‘yan Boko Haram suka sace a watan da ya gabata

- An tura sakon ta hanyar whatsapp akace ‘ya ku ‘yan duniya kuji tsoron Allah, ku daina bin Daghootu’

An fara samun sakonni daga Sambisa ta wayar wata budurwa da suka tafi da ita bayan harin Rann
An fara samun sakonni daga Sambisa ta wayar wata budurwa da suka tafi da ita bayan harin Rann

Anyi amfani da wayar hannu ta salula ta daya daga cikin matan da ‘Yan Boko Haram suka sace, an tura sako mara dadi ga lambobin ciki wayar.

Hauwa Liman, wadda aka dauka ma’aikaciyar hukumar bada taimakon farko ga marasa lafiya ce, wadda ‘yan Boko Haram suka sace a watan da ya gabata, bayan da suka kai hari a wani sansanin ‘yan gudun hijira, a Rann, jihar Borno.

A kalla mutane sha biyu wadanda suka hada da jami’an tsaro ne aka kashe, a lokacin harin tare da jami’an ICRC, biyu dasu kuma aka sace. A ranar Alhamis, anyi amfani da wayar, Malama Hauwa Liman, an tura sakon whatsapp zuwa wasu daga cikin lambobinta.

DUBA WANNAN: Bashi da ake bin kasar nan ya fara kaiwa kololuwa

Inda aka rubuta, “Ya ku ‘yan duniya, kuji tsoron Allah, ku daina bin taghootu”. Idan kuma ba haka ba, Allah zai daura mu akan ku, kuma zaku kasance tubabbu”.

Yawancin mutanen da abokai da suka ga wannan sako sun gogeshi, don basu yadda cewa itace ta tura sakon ba. Wata kawarta tace, “bata magana da hausa haka”.

An dai kai harin a sansanin soji na Rann inda aka fara jiyo sautin uryar wata budurwa kafin mayakan su iso kanta.

Sudai Boko Haram sunce baza su daina hari ba sai addininsu na Islama ya mulki Najeriya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng