Hukumar Yansandan Najeriya ta kammala shirye shiryen diban sabbin Yansanda 6,000
Shugaban hukumar ma’aikatan Yansandan Najeriya, Mike Okiro ya bayyana cewa hukumarsa ta kammala shirin daukan sabbin jami’an Yansanda guda 6,000 masu mukamin kurtu nan bada dadewa ba.
Okiro ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da jaridar Daily Trust, inda yace: “Babu wani rudani da aka samu, tunda dai aikin hukumar ya hada da daukan ma’aikata, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya tabbatar.”
KU KARANTA: Kotu ta daure mutane 63 da aka kama da hannu dumu dumu cikin rikicin jihar Kaduna
Majiyar Legit.ng ta jiyo Okiro na cigaba da karin haske in yake cewa; “Kundin tsarin mulki ya daura nauyin daukan sabbin Yansanda, basu mukamai dakuma hukunta duk wani jami’in hukumar da yayi ba daidai ba, banda babban sufetan Yansanda.”
“A yanzu haka mun kammala duk wasu shirye shirye da mataimakin sufetan Yansanda mai kula da bada horo na yadda za’a gudsanar da wannan muhimmin aiki, kamar yadda muka yi a shekarar 2016.” Inji shi.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito a kwanakin baya ne dai Okiro ya aika ma babban sufetan Yansanda, inda yake kalubalance shi akan wata sanarwa da rundunar Yansandan Najeriya ta fitar na daukan aiki, inda ya bayyana masa cewa ba huruminsa bane yin hakan, aikin hukumar ma’aikatan Yansanda ne.
Dayake karin haske game da cin hanci da rashawa da ya dabaibaye aikin Yansanda, sai yace ba laifin Yansanda bane, kuma ba irin horon da ake basu ba kenan, amma halayyar jama’a ne ya kawo haka. “Idan kaje kasashen waje zaka cewa ana girmama Yansanda, amma a Najeriya kowa ya tsani Yansanda.” Inji shi
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng