Kasar Saudiyya ta ce zata kera Makamin Nukiliya muddin kasar Iran ta kera

Kasar Saudiyya ta ce zata kera Makamin Nukiliya muddin kasar Iran ta kera

- Tashin tashinar dake tsakanin kasar Saudiyya da Iran ta yi tsamari

- Yanzu haka kasar Saudiyya ta ce ita ma zata kera nata makamin Nukiliyar

- Yariman kasar mai jiran gado shine ya bayyana haka a wata hira da yayi a tashar talabijin na CBS

Kasar Saudiyya ta ce zata kera Makamin Nukiliya muddin kasar Iran ta kera
Kasar Saudiyya ta ce zata kera Makamin Nukiliya muddin kasar Iran ta kera

A jayayyar dake tsakanin kasar Iran da kasar Saudiyya, kasar Saudiyya ta ce muddin aka bar kasar Iran ta kera makamin nukiliya to ba makawa ita ma sai ta kera.

DUBA WANNAN: Atiku Abubakar zai yi magana akan yadda za a farfado da tattalin arzikin Najeriya a birnin Landan

Yariman kasar Saudiyya mai jiran gado, Muhammed bin Salman, yayi kira ga shugaban malaman addinin kasar Iran "Hitila", ya ce muddin kasar Iran ta kera makamin nukiliya to babu makawa ita ma sai ta kera.

Ya ce: "Kasar Saudiyya bata bukatar mallakar makamin Nukiliya, amma ta ce babu kokonto muddin idan kasar Iran ta kera makamin, to muma zamu bi hanyar da suka bi mu kera, ba tare da wani bata lokaci ba," inji Yarima Muhammed, a wata hira da yayi da tashar gidan talabijin na CBS dake kasar Amurka ta yi dashi, kuma tashar ta ce zata nuna wa duniya abinda Yariman ya ce a cikin wani shirin ta na, a ranar Lahadi dinnan.

A wata hirar da tashar ta fitar a yau Alhamis, Yariman ya ce, yanda ake tunkarar shugaban kasar Iran din dai dai ya ke da yadda duniya a da ta tunkari Hitler, a lokacin da akidar take tashe a kasar Jamus.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng