Duk lokacin da na dawo gida sai mijina ya shinshina dan kamfai na - Wata mata ta shaidawa kotu

Duk lokacin da na dawo gida sai mijina ya shinshina dan kamfai na - Wata mata ta shaidawa kotu

- Wata kotu a jihar Legas ta katse igiyar wani aure mai shekaru 30 bisa zargin cin amana

- Kotu ta raba auren ne bayan mijin matar mai shekaru 88 ya koka kan cewar ya gaji da cin amanar aurensu da matar sa ke yi

- Alkaliyar kotun, Funmi Adeola, ta ce ma'auratan kan iya kama hanyoyi daban-daban domin yanzu babu aure a tsakaninsu

Wata kotu a Ikorodu dake garin Legas ta warware wani aure mai shekaru 30 bisa zargin cin amanar aure da mijin ke yiwa matar sa.

Kotun ta katse igiyar aure tsakanin ma'auratan bayan da mijin matar, Gbeminiyi Adeyiga; mai shekaru 88, ya shaidawa kotu cewar ya gaji da cin amanar aurensu da matar sa ke yi tare da rokon kotun ta warware auren.

Duk lokacin da na dawo gida sai mijina ya shinshina dan kamfai na - Wata mata ta shaidawa kotu
Duk lokacin da na dawo gida sai mijina ya shinshina dan kamfai na - Wata mata ta shaidawa kotu

Alkaliyar kotun, Funmi Adeola, ta ce yanzu ma'auratan kan iya kama hanyoyi daban-daban domin yanzu babu aure a tsakaninsu tunda ta tabbata cewar basu da bukatar sulhunta rikicin dake tsakaninsu.

Sai dai alkaliyar ta shaida ma su cewar dole su hada kai wajen daukan dawainiyar yaran da su ka haifa tare da yin gargadi gare su cewar kada su bari mutuwar aurensu ta shafi rayuwar yaransu.

DUBA WANNAN: Badakalar miliyan N450: Kotu ta yankewa tsohon ma'aikacin banki hukuncin daurin shakaru 12

Adeyiga, mazaunin gida mai lamba ta uku dake kan titin Munirat Aleje a Ikorodu ta garin Legas, ya shaidawa kotu cewar matar sa na kwanciya da maza daban-daban kuma ba ta kulawa da shi. Kazalika, ya shaidawa kotun cewar wasu lokutan har marinsa matar ke yi.

Saidai matar, Sakinat; mai shekaru 55 ta musanta dukkan zargin da mijinta ke yi mata tare da shaidawa kotun cewar bata son auren nasu ya mutu.

Rahoton kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya ce kotun ta raba auren duk da rokon Sakinat na son a yi masu sulhu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng