Atiku Abubakar zai yi magana akan yadda za a farfado da tattalin arzikin Najeriya a birnin Landan
-Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, zai yi jawabi akan tattalin Arziki a birnin Landan
-A ziyarar da ya kai kasar Ingila, tsohon mataimakin shugaban kasar, zai yi jawabi akan hanyar da za abi domin farfado da tattalin arzikin Najeriya
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, zaiyi jawabi akan tattalin arziki, a Royal Institute of International Affairs (Chatham House) dake birnin Landan da misalin karfe 10 na safe, a ranar 25 da watan Afirilu 2018. Tsohon mataimakin shugaban kasar zaiyi bayani ne kan tsawaita hanyoyin kula da tattalin arziki, da kuma hanyoyin da za a bi wanda zasu taimaka wurin samar da mafita, hanyoyin da idan har anyi amfani da su za a samo mafita ga matsalar tattalin arzikin da ake fuskanta a Najeriya.
DUBA WANNAN: Cire Tillerson daga kujerar shi ba zai shafi alakar Najeriya da Amurka ba - In ji Gwamnatin Tarayya
A ziyarar da ya kai kasar Ingila, Atiku Abubakar, zai yi jawabi ne, akan dangantakar dake tsakanin Afurka da Birtaniya a fannin zuba jari. Zai yi jawabin ne tare da Dr Liam Fox, sakataren kasuwancin kasashen waje na Birtaniya, akan samo sabuwar hanya wacce zata bunkasa kasuwancin Afirka.
An samu matsaya akan wannan jawaban ne bayan haduwar Atiku Abubakar da Dakta Liam Fox a watan Yuli shekarar 2017, da Firaminista Theresa May, inda suka zanta kan shawarwarin da kasar Ingila ta bayar akan bunkasa kasuwanci a Najeriya.
Atiku Abubakar, yana daya daga cikin mayan ‘yan kasuwan Najeriya masu dogaro da kansu, da kuma son ganin ya kawo cigaba ga al'ummar Najeriya.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng