An kama wasu mutane 4 da laifin kashe abokin su a jihar Filato
- An gurfanar da wasu mutane 4 a ranar Larabar nan a gaban kotun jihar Filato bisa zargin kashe abokinsu
-Wadanda ake zargin sun kasheshi ta hanyar daba masa wuka a lokacin da fada ya kaure a tsakanin su
A ranar Larabar nan ne aka gurfanar da wasu mutane hudu a gaban babbar kotun Filato dake jihar Jos bisa zargin kashe abokinsu, mai suna Joseph Gonsum.
DUBA WANNAN: Jerin kasashen da suka fi ko ina dadin rayuwa a duniya
Wadanda ake zargin Terry Kefas, Samson James, Emmanuel Jah, da kuma Patrick Nyam, duka ‘yan Kauyen Gada Biyu ne, ana zargin su da dabawa wuka Gonsum, a lokacin da fada ya rincabe a tsakanin su.
Majiyar mu Legit.ng ta taba kawo muku rahoton inda aka fara shari'ar wanda ake zargin tun a ranar 22 ga watan Satumbar shekarar 2017. Ana zarginsu da aikata laifin kisa kai wanda matakin sa a shari'a hukuncinsa kisa ne.
Mai gabatar da kara, Mista N.S Miner, ya fadawa kotu cewa wadanda ake zargin sun aikata laifin a ranar 25 ga watan Disamba 2016. Sannan ya kara bayyanawa kotu cewa wadanda ake zargin sun rike wukake inda suka daba masa a ciki, hakan yayi sanadiyar mutuwarsa. A karshe da bincike ya tsananta, wadanda ake zargin sun amsa laifin su, inda suka tabbatar wa da kotu cewa sun aikata laifin.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng