Kyakkyawar shaidar da manyan masanan Yahudu da Nasara suka yiwa Manzo (SAW)
- Annabi Muhammadu (SAW) an shaide shi da gaskiya, rikon amana, tausayi, kyauta da sauran su
- Abinda yasa wasu manya daga cikin Yahudawa da Nasara suka mashi kyawawan shaidu
Kyakkyawar shedar da wasu manyan masanan Yahudu da Nasara su ka yiwa Manzo (S.A.W)
Manzon Allah (SAW) shine annabin da Allah ya aiko wa masu bin addinin musulunci, sun kuma yarda dashi da gaskiya, Allah ya turo shi sama da shekara dubu da suka wuce, amma duk da haka al'ummar musulmi sun yarda dashi, saboda sun yarda cewar baya karya, kuma sun aminta da cewa addinin su shine addinin gaskiya,
Da yawa daga cikin masu bin addinin Kiristanci suma sun yadda dashi, musamman ma manyan malaman su da kuma wanda suka karanci addinin da kyau sun yadda cewa mai gaskiya ne, yana kuma da rikon amana, baya zalunci da cuta. Hakan nema yasa wasu manya daga cikin Yahudu da Nasara suka yi masa wata kyakkyawar shaida. Inda kowanne a cikin su yake cewa:
DUBA WANNAN: Atiku Abubakar zai yi magana akan yadda za a farfado da tattalin arzikin Najeriya a birnin Land
- Fiodor Mikhaïlovitch Dostoïevski
Wani shahararren marubucin kasar Rasha, wanda aka haifa 30 ga watan Oktoban shekarar 1821 a Moscow, ya bar duniya 28 ga watan Janairu 1881 a Saint-Pétersbourg ya bayyana cewa:
"Manzon Allah ya je sararin subhana, ya kuma gana da Ubangijin al arshi. Saboda haka ko shakka ba bu, na yi imani da Isra'i da Mi'iraj."
2. Goethe:
Shahararren marubuci, kuma kwararre a bangaren adabi da harkar siyasa a kasar Jamus, an haife shi 28 ga watan Agusta a shekarar 1749 a Frankfurt, sannan ya mutu a birnin Weimar, yace :
"Annabi Muhammad ya yi abin da ba bu wani mutum bature da ya taba yin sa, duk da irin cigaban da muke dashi a bangaren ilimin fasaha da kimiyya. Ba bu wanda ya isa ya kamo shi. Na bincika duk a tarihin duniya, don na samo wanda zan misalta shi dashi, amma ban ga kamar Muhammad ba".
3. Alphonse de la Martine:
Shahararren marubuci, sannan kuma babban masani a fannin siyasa a kasar Faransa , an haife shi 21 ga watan Yulin shekarar 1790 a Macon, kuma ya bar duniya ranar 28 ga watan Fabrairu a shekarar a 1869 a birnin Paris, yace :
" Inda girman makoma, rashin kayan aiki, da kuma gagara misalin nasara za su kasance ma'aunan ilimin ga bil adama, wa ya isa ya kwatanta kansa da Muhammad, mafificin mutum, wanda zuciyar sa ke cike makil da rahama, ko shakka ba bu ba a taba kamar sa ba, kuma ba za a taba yin kamar sa ba har duniya ta tashi".
4. Léon Nikolajeviç Tolstoï:
Dan kasar Rasha, an haife shi 9 ga watan Satumban shekarar 1828 a Yasnaya Polyana, sannan ya bar duniya a birnin LevTolstoy a ranar 20 ga watan Nuwamban shekarar 1910, yace :
"Annabi Muhammad ya fi karfin a kirashi Manzo, domin kuwa ya kasance daya daga cikin mutanen da suka sauya fasalin duniya. Ya fito da al'ummarsa daga bakin duhu ya zuwa haske, daga kasa ya zuwa sararin samaniya. Hakan ne yasa ya kamata a yaba masa. Ya haramta zubar da jini wadanda ba su ji ba basu gani ba, ya bude kofofin cigaba da yalwa ga al'umma. Babu wanda ya taba yin irin wannan abun gabanin sa, kuma baza ayi ba a bayansa. Girmama wa, martaba da daukaka su tabbata a gare shi".
5. Thomas Carlyle:
Shahararren marubuci, kuma kwararren a bangaren tarihi a kasar Scotland, an haife shi 4 ga watan Disamba shekarar 1795 a Ecclefechan, sannan ya bar duniya 5 ga watan fabrairu shekarar 1881 a birnin Landan, yace :
"Bai kamata ba, abinda wasu suke yi na daukan Musulmai, da cewar suna bin addinin karya. Sannan kuma bai kamata ba ganin yadda kowa ke daukar Muhammad da cewa shi Manzon karyane. Duk duniya kowa ya shaida cewa a duk tsawon rayuwar da yayi, Muhammad ya kasance mutum mai kafa dokoki na wadanda ba za su ta ba rushewaba, mutum ne mai farar aniya, ga kankan da kai, ga kunya, ga kyauta, ga tausayi, ga imani, gashi kamilin mutum kuma amintacce".
6. Napoléon Bonaparte:
Sarkin daular Farisa, an haife shi a shekarar 1769 a Ajaccio, sannan ya bar duniya 5 ga watan Mayis shekarar 1821 a Longwood, yace :
"Addinin Musulunci ya yi watsi da bautar gumaka. Bai yarda da wani abin bauta ba face Allah mai girma, Muhammad kuma manzon sa ne, kalmar nan ita ce ginshikin addinin Musulunci. Muhimman abubuwan da za mu fahimta a nan shine, ya kara tabbatar da kalmar Annabi Musa wacce Yesu Al Masihu ya jaddada. Ina fatan wata rana zan yi nasara akan hada kawunan dukannin masana da masu ilimin kasata karkashin inuwar Al Kur'ani mai girma".
7. George Bernard Shaw:
Wani shahararren marubuci a kasar Birtaniya , an haife shi 26 ga watan Yulin shekarar 1856 a Portobello, sannan ya bar duniya 2 ga watan Nuwamba shekarar 1950, yace :
"A yanzu abinda duniya ke so shine jagorancin mutum mai tunani irin na Muhammad. Kiristocin zamanin da, saboda da jahilci da tsattsauran ra'ayi irin nasu, sune suka dinga shafawa Muhammad da addinin sa bakin fenti. Sun bayyana addinin Musulunci a matsayin makiyin addinin Kirista. sai bayan dana bincika tarihin wannan mutumin, sai na gane cewar, shi ba makiyin Kirista ba ne, shi ya zo ne domin ya ceci duniya baki daya. A tunani na idan har zai mulki duniyar mu ta yanzu, to da zai warware dukannin matsalolin mu, sannan kwanciyar hankali, da wadata da farin ciki za su kasance a kowane wuri da ke doron duniya".
8. Mahatma K. Gandhi:
Tsohon shugaban kasar Indiya ,an haife shi 2 ga watan Oktoba shekarar 1869 a Porbandar, sannan ya bar duniya 30 ga watan Janairu shekarar 1948 a birnin New Delhi, yace :
"Ina matukar bukatar in zurfafa sani na akan rayuwar mutumin da ya samu kyakkyawar shaida a zuciyar milyoyin jama'a. Babu shakka na tattaba cewa ba karfin takobi ne ba yasa Muhammad ya shiga zuciyar mabiya addinin Musulunci ba. Babu kamar sa ta bangaren karamci, aminci da daraja na kasa dashi".
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng